
Wata sabuwar ƙungiyar ƴanta’adda da ake kira Wulowulo ta ɓulla a ƴankin arewa ta tsakiyar Najeriya, a dai-dai lokacin da ƙasar ke fama da ɗimbin matsalolin tsaro.
Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya bayyana haka yayin gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki a Lafia, ya kuma danganta sabuwar ƙungiyar da ‘yan Boko Haram.
Sule ya ce wasu daga cikin ‘ƴa’ƴan ƙungiyar na kai hare-hare a jihar Kwara da wasu ƴankunan dake arewa ta tsakiya.
Gwamnan ya kuma nemi haɗin kan jami’an tsaro domin daƙile ayyukan ƴanta’addan waɗanda suke bazuwa a jihohin dake yankin.
Sule ya ce ganin yadda ake fama da matsalar a jihar Kwara ya zama wajibi su gaggauta ɗaukar matakai da zummar ganin sun kare lafiya da dukiyoyin jama’ar su.
Gwamnan ya kuma bada umarnin gudanar da cikakken bincike a kan kisan da aka yi a ƙaramar hukumar Kokona, wanda ya shafi rayukan mutane 7 a rikicin fili tsakanin ƴan kabilar Mada da Ninzom.
Daga ƙarshe, gwamnan ya nemi shugabannin hukumomin tsaron da su tashi tsaye a kan masu garkuwa da mutane a ƙananan hukumomin Lafia da Karu.