Shugaban ya kuma yi alkawarin kara hutun bakukuwan sallah daga kwana daya zuwa kwanaki biyu
Shugaba John Mahama ya ce domin saukaka wa Musulmin Ghana, ya kuma kafa kwamiti na musamman don gudanar da wannan aiki
Kwamitin zai tafi kasar Saudiyya ranar Litinin domin tattaunawa yin ragin ga mahajjatan kasar.
Mista Mahama ya sanar da aniyarsa ta rage kudin kujerar aikin Hajji, ya kuma ce, ya kafa kwamiti na musamman kan hakan.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin addu’o’i na musamman da aka gudanar a Babban Masallacin Accra a ranar Juma’a.
Ya kuma ce Kwamitin zai tafi Saudiyya ranar Litinin domin tattaunawa da hukumomin kasar domin yiwuwar rage kudin aikin hajjin.
TRT ta rawaito cewa, shugaban ya kuma sanar da aniyarsa na karin kwana daya a yayin shagulgulan bikin karamar Sallah.
Idan karin ya tabbata, hakan zai bai wa Musulman Ghana damar samun hutun kwanaki biyu domin gudanar da shagulgulan Sallah karamar da babba a maimakon kwana guda.
Mista Mahama ya ce, za a yi wannan gyaran na karin hutun Sallah da zarar Majalisar Dokokin kasar ta soma zama.
Mista Mahama ya jaddada kudirin gwamnatinsa ta bangaren cika alkawuran da ta dauka ga al’ummar Musulmi a lokacin yakin neman zabe.
A ranar 7 ga watan Janairu ne aka rantsar da sabon shugaban ƙasar na Ghana John Dramani Mahama bayan ya lashe zaɓen ƙasar wanda aka gudanar 7 ga watan Disamabar 2024.
Mahama ya maye gurbin Nana Akufo-Addo, wanda ya sauka bayan kammala wa’adi biyu na shugabanci.