An zabi tsohon Minista Kabiru Tanimu Turaki (SAN), a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar (PDP) na ƙasa.
An zaɓi Turaki ne a babban taron jam’iyyar da ake gudanarwa a filin wasa na Lekan Salami da ke Ibadan, Jihar Oyo, inda wakilai daga jihohi 17 suka jefa ƙuri’un su domin zaɓen sabbin shugabannin jam’iyyar na ƙasa.
Tsohon Sanata Ben Obi daga Anambra shi ne ya bayyana sakamakon zaben, inda ya ce Turaki ya samu ƙuri’u 1,516, ya kayar da Sanata Yakubu Danmarke wanda ya samu ƙuri’u 275.
Ya ƙara da cewa jimilla an jefa ƙuri’u 1,834 a zaben, amma an samu ƙuri’u 43 da aka soke.
Obi ya kuma bayyana Solarin Adekunle a matsayin wanda ya lashe kujerar Mataimakin Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa.
Kujeru biyu ne kawai aka yi takara a kansu. Daga cikin wakilai 3,131 da aka tsara, an tantance 2,745.
Jim kadan bayan ayyana shi a matsayin wanda yayi nasara, Turaki ya tabbatar wa yayan jam’iyyar cewa ba zai ci amanarsu ba, kuma zai sauke nauyin da aka ɗora masa.
Tun a jiya dai Jamiyyar ta anar da korar tohon gwamnan Rivers kuma ministan Abuja Nyesom Wike da wasu mutane bayan an zarge su da yiwa jamiyyar makarkashiya.
