
Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, yayi kira da cewa matsalolin yara da ba sa zuwa makaranta a ƙasa zasu iya kawo sabbin ta’addanci irin na Boko Haram a nan gaba, idan ba a magance su ba yanzu.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a jihar Bauchi a ranar Talata.
“ƙarfin ƙasa ya dogara ne akan ci gaban ɗan adam da ƙarfafa masa Kuma da samar da ayyuka, ba kawai gine-gine ba.” in ji shi.
Tsohon shugaban da yayi wa’adi biyu, ya kuma yi kira ga hukumomi a duk matakai da su haɗa hannu don magance matsalar yara da ba zuwa makaranta.
Wanda yawansu ya kai fiye da miliyan 20—wato kashi 10% na jama’ar ƙasa baki daya.
Ya kuma ƙara da cewa “Bankan Duniya ya ce muna da yara fiye da miliyan 20 da ya kamata su kasance a makaranta amma ba sa zuwa, Wanda hakan na da nasaba da ƙirƙirar sabbin Boko Haram a gobe, wanda bama bukatar ganin hakan.” In ji shi.
A lokacin taron ya yaba wa gwamnan jihar Bala Mohammed kan ayyukan ci gaba, amma ya jaddada cewa ilimi shine mabuɗin kare ƙasa.
Obasanjo ya kuma ƙaddamar da rarraba na’urori 10,000 ga mutanen daga yankin Arewa-Maso-Gabas, Olusegun Obasanjo, tare da haɗin kai da Starkey Hearing Foundation.