
Rundunar ‘Yansandan Jihar Neja, ta kashe masu garkuwa da mutane uku a wani samame da ta kai dajin Kokolo, Nasko a ƙaramar hukumar Magama, a ranar 12 ga watan Satumba, 2025.
Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda sun yi musayar wuta da masu garkuwar kafin a kashe su.
Sun ceto mutum ɗaya da aka sace, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
An kuma samu bindigogi ƙirar AK-74 guda biyu da harsashi 49 daga maɓoyarsu.
A wani samame daban a ranar 25 ga watan Satumba, sashen Anti-Thuggery Unit ya kai farmaki maɓoyar masu laifi a Sabon-Titi, Tunga, Minna, inda aka kama wasu ɓarayi biyu.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Murtala Abbas mai shekaru 18 daga Katsina da kuma Hassan Ibrahim mai shekaru 20 daga Tunga.
An kama su da makamai irin su adduna, bindigogi ƙirar gida, kayan ‘yansanda da miyagun ƙwayoyi.