
Rundunar tsaro ta Civil defence ta tabbatar da cewa wasu mahara sun kai farmaki kan jami’anta inda suka kashe guda takwas daga ciki a wani harin kwantar ɓauna da suka kai musu.
Rundunar ta ce an kai harin ne kan jami’anta a garin Okpella da ke ƙaramar hukumar Etsaka ta Gabas a jihar Edo a kudancin Najeriya a ranar 5 ga watan Satumba.
Kakakin rundunar, Afolabi Babawale ne ta tabbatar da aukuwar lamarin, kamar yadda tashar NTA ta gwamnatin Najeriya ta ruwaito.
Ya ce jami’an na NSCDC suna aiki ne domin ba wasu ƴan ƙasar China kariya a wani kamfani mallakin BUA da suke aiki, sannan ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin ƴan Chinan guda biyar ya ɓace, amma ya ce jami’an nasu na yin iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin sun ceto shi.