Aƙalla mutane 40 ne suka mutu a wani harin jirgin sama mara matuƙi da rundunar RSF ta kai a yankin Kordofan ta Arewa da ke tsakiyar Sudan, a cewar wani jami’in yankin.
Kungiyar ta kai hari ne a ranar Litinin, a cewar Kwamishinan kula Da Harkokin Jinƙai na yankin Kordofan ta Arewa, wanda ba a bayyana sunansa ba.
Kwamishinan ya shaida wa kafar Al Jazeera cewa mace-macen sun faru ne a harin da aka kai wa fararen hula a ƙauyen Al Luweib da ke gabashin babban birnin lardin El Obeid.
A baya, gwamnatin jihar ta ce, an kashe fararen hula da dama, ciki har da yara da mata, a harin da aka kai wa wani tantin zaman makoki a ƙauyen.
Gwamnatin jihar ta yi kira ga al’ummar duniya da su gaggauta ayyana RSF a matsayin “ƙungiyar ta’addanci”, tana mai zarginta da “aikata laifukan kisan kare-dangi kan fararen hula marasa makamai”.
Tun dai daga ranar 15 ga Afrilun 2023, ƙasar Sudan ta fada yaƙin da har yanzu masu shiga tsakani daga yankin da ƙasashen waje suka gaza kawo ƙarshensa.
