
Kwamitin ya gamsu da irin yadda shugaban ke gudanar mulkinsa musamman yadda yake farfado da tattalin arziki, inji Sanata Barau Jibrin
Kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC ya amince wa shugaba Bola Tinubu ya nemi wa’adi na biyu a shugabancin kasar nan.
Manyan shugabannin jam’iyyar sun yanke wannan shawarar ne a babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a ranar Laraba a Abuja.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Barau Jibrin ya bayyana dalilinsu na amincewa da yin tazarcen a hirarsa da manema labarai
“…. Shugaban kasa ya zama mai basira inda ya fito da yanayi wadanda suka farfado da tattalin arzikin wanda a yanzu an daina rantar kudi a wurin CBN kuma kudin shigar da ake samu ya karu
“Kuma man da ake hakowa wanda a da, bai kai ganga miliyan daya ba 800, 700 amma yanzu har ya kai ganga Miliyan 1 da 700 a kowacce rana. Hatta jihohi ma kudin da suke samu ya ninka hara sau uku.” in ji Sanata Barau
Shugaban kungiyar gwamnonin APC Hope Uzodinma ne ya gabatar da kudirin amincewa da Tinubu ya dora da shugabancin kasar nan a zango na biyu a 2027 wanda kuma hakan ya samu amincewar sauran ‘yan kwamitin