
wasu mutane biyu sun mutu, Uku sun Jikkata a wani hari da aka kai kan tarin yahudawa a Birtaniya.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a Heaton Park a garin Manchester.
Rahotanni sun nuna cewa, biyu daga cikin Yahudawan da aka Kai hari sun mutu, wasu uku kuma na cikin mummunan hali, sakamakon wani hari da wani mutum cikin mota ya kutsa cikin taro masu bautar tare da yin amfani da wuka kan masu taron na majalisar Yahudu da ke bauta ta Heaton Park Hebrew Congregation a yankin Crumpsall a birnin Manchester, arewacin Ingila.
Harin ya faru ne a lokacin bikinsu na Yom Kippur, ranar ta musamman a cikin kalandar Yahuduwa, inda yawancin jama’a ke kalubalantar taron.
Da misalign karfe 9:31 na safe, ‘yan sandan Greater Manchester Police (GMP) sun sami kira daga cikin masu bautar wanda ya ce, ya ga wata mota da wani direba ke yin tukin ganganci ya kuma nufi dandazon mutanen, tare da cakawa wani mutum a cikin taron wuka.
‘Yansandan sun Isa wurin cikin gaggawa sun kuma samu nasarar harbe Wanda ya kai harin, da ya hallaka shi nan take.
An garzaya da mutane hudu zuwa asibiti, an kuma tabbatar da biyu sun mutu, kuma uku na cikin wani mawuyacin hali sakamakon harin.
Harin kan Yahudawan ya zo a lokacin da al’ummar Yahudu a Birtaniya ke fuskantar ƙaruwar barazana tun daga harin Hamas kan Isra’il a Oktoba 2023, tare da rahotannin haɓakar tashin hankali a yankin Gaza.