Masu Sa-ido na Cikin Gida da Na Waje Sun Koka Kan Sayen Kuri’u da Karancin Fitowar Masu Kada Kuri’a a Zaben Anambra
Masu sa-ido na kasa da kasa da na cikin gida sun bayyana damuwa kan yawaitar sayan kuri’u da kuma karancin fitowar masu kada kuri’a* a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 8 ga Nuwamba a jihar Anambra.
Cikin rahoton da YIAGA Africa, hadin gwiwa da EU-SDGN II da sauran abokan hulɗa suka fitar, sun nuna cewa yawancin runfunan zabe a ƙananan hukumomi 21 na jihar sun fuskanci ƙarancin masu kada kuri’a.
Samson Itodo, Daraktan YIAGA Africa, ya bayyana cewa sayan kuri’u da ƙarancin fitowar jama’a na daga cikin manyan matsaloli da aka fi fuskanta.
Asabe Ndahi daga Kukah Centre ta nuna damuwa kan gurbacewar tsaro da jinkirin isowar jami’an INEC da na tsaro, musamman a wurare masu hadari irin su Nkwelle-Ezunaka, Ihiala, Ogbaru da Nnewi South. Ta kuma ce an samu rahoton sayan kuri’u da tsoratar da masu kada kuri’a a wasu kananan hukumomi.
Haka zalika, CDD-West Africa ta bayyana irin wannan damuwa.
Duk da haka, YIAGA ta ce rahotannin daga wakilanta a rumfunan zabe 250 sun nuna cewa kashi 85 cikin 100 sun fara tantancewa da kada kuri’a da wuri, yayin da kashi 86 cikin 100 suka samu na’urar BVAS.
