Rahotanni daga yankin Adamawa ya bayyana cewa ana ci gaba da kama mutane musamman magoya bayan ‘yan adawa biyo bayan zanga-zangar rashin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar.
Hakan na zuwa ne duk ikirarin Ministan Kula Da Al’amuran Cikin Gida na kasar na sakin mutane kusan 60 da aka kama.
Ministan ya ambata sakin mutanen da aka kama a Ngaoundere sakamakon rikicin da ya ɓarke ranar 12 ga Oktoba, bayan zaɓen shugaban ƙasar mai cike da ce-ce-ku-ce da aka yi.
Minista
, ya fadi hakan ne a lokacin ziyarar aiki da ya kai babban birnin jihar Adamawa a ranar Litinin.
- Sojoji sun daƙile harin da ƴan ta’addan ISWAP a iyakar Najeriya da Kamaru
- Jagoran Adawa ya ayyana nasara a zaben shugaban kasar Kamaru
“An kama mutane 136 dangane da rikicin, amma an saki 60 daga cikinsu galibi yara ƙanana bisa ƙarƙashin kulawar iyaye.
“Har yanzu ana tsare da sauran mutanen saboda abin da hukumomi suka bayyana a matsayin yunƙurin tayar da hankali da kuma ɓarnata dukiyar ƙasar”. In ji shi.
Matatakin kama mutanen ya biyo bayan wa’adin sa’o’i 48 da madugun ‘yan adawa Issa Tchiroma Bakary, ya bayar, wanda ya bukaci a saki dukkanin mutanen da aka tsare ba bisa ka’ida ba.
Duk da cewa Atanga Nji bai ambaci bukatar Tchiroma kai tsaye ba, masu lura da al’amura na kallon sakin wani bangare a matsayin wata alama da ke nuna cewa matsin lambar da ake yiwa gwamnati na ci gaba da yin tasiri.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam na ci gaba da yin Allah wadai da matakan gwamnatin, tare da yin kira da a saki dukkanin waɗanda ake tsare da su.
