Wani matashi ya rasa ransa bayan wani rikici da ya samo asali da soyayya tsakaninsa da wata budurwa.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Gurdadi, cikin Karamar Hukumar Yusufari a Jihar Yobe ga Jibrin Saidu Lamido dan shekara 20.
A Rahotannin da muka samu, lamarin ya faru ne a ranar Talata, lokacin da Jibrin ya je ziyarar budurwarsa Saratu Gata, mai shekaru 22, a ƙauyen Kalameri.
A yayin da suke tare, wani mutum da ba a gano ko wanene ba, ya zo wurin, ya kuma tafi da budurwar.
Daga baya kuma aka ce, ya dawo ya kalubalanci Jibrin da ya biyo su idan yana ganin shi namijin gaske ne.
Daga nan ne rikici ya ɓarke tsakaninsu, inda wanda ake zargi ya daɓa wa Jibrin adda a wuya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Yobe ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ce ta mika gawar mamacin ga iyayensa domin gudanar da jana’izarsa.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, ya bayyana cewa ana ci gaba da bincike da neman wanda ake zargi, wanda ya tsere daga yankin bayan aikata laifin.
