Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a kan hana shi samun takardar tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar PDP.
Sule Lamido bai samu damar sayen form ɗin ba daga shalkwatar sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a gaban magoya bayansa, tsohon gwamnan ya nuna rashin gamsuwarsa kan matakin.
Sule Lamido ya ce, a shirye yake ya tsaya takarar shugabancin jam’iyyar a zaɓen da za a yi lokacin babban taron jam’iyyar na cikin watan Nuwamban a jihar Oyo.
Tsohon gwamnna ya sha alwashin tafiya kotu idan har aka ƙi sayar masa da Takardar tsayawa takarar.
Tuni dai gwamnonin PDP suka nuna goyon bayansu ga tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Turaki a matsayin shugaban jam’iyyar.
