Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, za ta kawo ziyara jihar Kano domin ƙaddamar da shirin bunƙasa sana’o’i, fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire a yankin Arewa maso yamma.
Wannan na cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Kano, Comr. Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar.
Sanarwar ta ce za a gudanar da taron daga ranar 23 zuwa 25 ga watan Afrilu 2026.
Ya ce shirin na da nufin tallafawa matasa da mata wajen bunƙasa sana’o’i da fasaha domin ƙarfafa tattalin arziki.
Kwamishinan ya kuma gayyaci al’umma musamman mata da su fito domin tarbar uwargidan shugaban ƙasar da kuma cin gajiyar shirin.
