Aminu Abdullahi Ibrahim
Mai taimakawa gwamnan Kano kan inganta ilimi Malam Haladu Muhammad, ya ce a makarantun firamare na Kano akwai dalibai fiye da miliyan 4 da rabi yayin da a kanana da manyan makarantun sakandire daliban basu wuce miliyan daya ba.
Ya bayyana haka ne yayin wani taron tattaunawa kan hanyoyin inganta koyo da koyarwa da Gamayya kungiyoyi masu rajin ganin ilimi ya tafi daidai a Kano ta shirya a wani bangare na ranar ilimi ta Duniya da ake gudanarwa a Asabar din nan.
Ya ce rashin isassun ajujuwan karatu na daga cikin matsalolin da suka haifar da karancin dalibai a makarantun sakandire.
Malam Haladu yakara da cewa wannan dalilin ne yasa gwamnati ta himmatu wajen gina sabbin ajujuwa tare da gyara wadanda ake da su.
Ya ce malaman makaranta da ake da su ba su wuce dubu 50 ba duk da daukar sabbi da gwamna Abba Kabir Yusuf amma har yanzu ana bukatar malamai a kalla dubu 80.
A nasa bangaren sakataren kwamitin al’umma gatan makaranta (SBMC) Ibrahim H Sale, ya ce kwamitin SBMC su n a taka rawa wajen tabbatar da koyo da koyarwa mai inganci a jihar Kano.
Da yake jawabi shugaban gamayya kungiyoyi masu rajin ganin ilimi ya tafi daidai a Kano Dr. Auwalu Halilu, ya ce gwamnati da kungiyoyi kadai ba zasu iya kawo sauyi ba har sai al’umma sun bayar da gudunmawa.
Ya ce al’umma suna da rawar da zasu taka wajen tallafawa gwamnati don a tabbatar ilimi ya tafi daidai.
Dr. Auwalu Halilu ya ce idan an ce gwamnati to al’umma ake nufi dole ne mutane su gamsu cewa makarantun gwamnati na su ne.
Ya ce suna sa ran cewa a taro nag aba da zasu gudanar za a ga sauyi sosai a tsarin ilimin jihar Kano.
