
Ramadan wata ne mai alfarma da Musulmai ke cinyewa cikin ibada, azumi, da kuma neman gafarar Ubangiji.
A wannan wata mai daraja, ana ƙarfafa mutane su ƙara kusanci da Allah ta hanyar bautarSa, addu’o’i, da aikata kyawawan ayyuka.
A yayin da ake shiga goman tsakiya na watan Ramadan, wani malamin addinin Musulunci, Malam Muhammad Mahi Naniya, ya ja hankalin al’umma kan muhimmancin dagewa da neman gafarar Ubangiji.
A wata tattaunawa da ya yi da wakiliyar mu, Safina Abdullahi Hassan, Malam Muhammad Mahi ya bayyana cewa Ramadan wata ne da ke zuwa da falala daban-daban a kowane lokaci.
Malamin ya ƙara da cewa Musulmai su yi ƙoƙari wajen yawaita ayyukan alheri kamar bayar da sadaka, taimakon mabukata, da kuma ƙarfafa dangantaka da Allah ta hanyar salloli da karatun Alƙur’ani.

Ya ce, ba wai a cikin Ramadan kaɗai ake bukatar aikatawa ba, har ma da bayan kammala watan, domin hakan na da lada mai yawa.
A karshe, ya bukaci al’umma da su yi amfani da wannan dama ta tsarkake zuciya da neman gafarar Ubangiji, tare da ƙoƙarin dorewa da ayyukan alheri bayan kammala watan Ramadan