
Kungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC) ta zargi Jami’ar Adeleke ta Jihar Osun da hana dalibai Musulmi gudanar da ibadar Ramadan.
A wata sanarwa da Babban Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce jami’ar na tilasta wa dalibai Musulmi halartar shirye-shiryen Coci.
MURIC ta bayyana cewa ta samu korafe-korafe daga dalibai Musulmi na jami’ar, inda suka ce an hana su gudanar da ibada musamman a wannan wata mai alfarma.

Ƙungiyar ta bayyana hakan a matsayin tauye haƙƙin dalibai Musulmi da rashin mutunta addinin Musulunci, tana mai kira da a duba lamarin.
Farfesa Akintola ya ce tun a shekarar 2019 MURIC ke gabatar da irin waɗannan zarge-zarge kan jami’ar, inda ta bukaci Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) da ta binciki batun.