
Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Kano, (SUBEB), tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Bai-daya ta Ƙasa, (UBEC), sun ƙaddamar da gangamin sa yara a makaranta na shekarar karatu ta 2026/2027 a Masarautar Karaye.
Gangamin na da nufin ganin an shigar da dukkan yaran da suka kai shekarun makaranta, tare da dawo da yaran da ba sa zuwa makaranta cikin aji a faɗin ƙananan hukumomin 44 na jihar.
Da yake jawabi a madadin Babbar Sakataren UBEC, Mai kula da Shyar Kano a Hukumar UBEC, Malam Abdulrahman Musa, ya ce gangamin zai mayar da hankali ne wajen wayar da kan iyaye da al’umma su shigar da yaran da suka kai shekaru 6 zuwa 11 makaranta, tare da tabbatar da cewa yaran sun ci gaba da zuwa makaranta har su kammala karatunsu. Ya kuma jaddada muhimmancin bai wa ‘yan mata, yara masu nakasa da sauran yara masu rauni damar samun ilimi daidai da kowa.
Shi ma Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, wanda Mai Bai wa Gwamnan Jihar Kano Shawara kan Ilimi, Malam Haladu Muhammad, ya wakilta, ya yi kira ga iyaye, da al’umma, da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa hannu wajen dawo da yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ya ce ya kamata duk yaron da ya kai shekara shida kuma ya cancanci shiga aji ɗaya ya samu damar shiga makaranta a lokacin da ya dace. Ya kuma tabbatar da cewa Ma’aikatar Ilimi za ta ci gaba da aiki tare da al’umma da sarakunan gargajiya domin inganta harkar ilimi da kuma ci gaba da nasarorin da aka samu.
A nata jawabin, bakuwa mai jawabi, Farfesa Aisha Abdul Ismail, ta bukaci masu ruwa da tsaki da su gano tare da magance matsalolin da suke hana yara zuwa makaranta.
Ta jaddada cewa ba shigar da yara makaranta kawai ake bukata ba, har da tabbatar da cewa sun ci gaba da zuwa makaranta har su kammala. Ta kuma bukaci kowa ya zama “Jakadan Shigar da Yara Makaranta”, ta hanyar wayar da kan al’umma, da gano yaran da ba sa zuwa makaranta da taimaka musu su koma makaranta su sami ilimi don zama jakadu nagari a nan gaba.
Da yake nasa jawabin, Sarkin Karaye, Mai Martaba Muhammad Maharaz, ya bukaci iyaye da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa yara sun shiga makaranta, sun ci gaba da zuwa kuma sun kammala karatunsu. Ya kuma yi kira ga UBEC da SUBEB da su ƙara ƙarfafa makarantun Ilimin Yara Makiyaya domin su ma su samu ingantaccen ilimi. Sarkin ya kuma umurci Hakimai, da Dagatai, da Masu Unguwanni da Limamai da su taimaka wajen yaɗa wannan saƙo a faɗin Masarautar Karaye.
A nasa ɓangaren, Mukaddashin Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta kuma Kwamishina na ɗaya a Hukumar, Hon. Wada Ibrahim Daho, ya yi kira ga iyaye da su shigar da ‘ya’yansu makaranta, yana mai yabawa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa ƙoƙarin da yake yi wajen bunkasa ilimi ta hayar gina sabbin makarantu da ajujuwa, da gyaran wadan da suka lalace, da samar da kujeru da kayan koyo da koyarwa, da kuma biyan albashi da ƙarin girma ga ma’aikatan ilimi a kan lokaci.
