
Bankin Duniya ya ce, tattalin arzikin Najeriya ya haɓɓaka fiye da kowanne lokaci cikin shekara goma da ta gabata.
Bankin ya ce hakan ya faru ne sakamakon wasu muhimman gyare-gyaren da gwamnati ta aiwatar sai dai kuma Bankin Duniyan ya gargadi cewa hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da addabar miliyoyin ƴan ƙasar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bankin Duniya ya fitar wa manema labarai, inda ya bayyana cewa ƙarfin tattalin arziƙin Najeriya na cikin gida ya ƙaru da kashi 4.6 cikin 100 a zangon ƙarshe na shekara ta 2024.
Bankin Duniya ya yaba wa gwamnatin shugaban Bola Ahmed Tinubu saboda ɗaukar matakan gyaran tattalin arziki tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.
Daga cikin wadannan gyare-gyare har da cire tallafin man fetur da ƙoƙarin farfaɗo da darajar Naira.