Farashin kayayyaki na faduwa a Najeriya a cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS.
Hukumar ta bayyana cewa farashin kayayyakin ya sauko zuwa kashi 16.05% a watan Oktobar shekarar nan, daga kashi 18.02% da aka samu a watan Satumba.
Rahoton hukumar ya kuma ce, adadin ya ragu da kashi 1.96% idan aka kwatanta da hauhawar farashin kayayyaki a watan Satumba na 2025.
Hukumar NBS ta kuma bayyana cewa a halin yanzu, karuwar farashin kayayyaki a watan Oktoba na 2025 ta ragu da kashi 13.12% idan aka kwatanta da wannan watan a shekarar da ta gabata.
Hukumar ta ce raguwar hauhawar farashin kayayyaki ya samo asali ne daga sauye-sauyen tattalin arziki da aka samu a shekarar da muke ciki.
