
Fitaccen ɗan siyasa kuma jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Abdulmajid Ɗan Bilki Kwamanda ya ce, ya yi nadamar mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2023.
Kwamanda ya ce, shugaba Tinubu ya watsar da waɗanda suka sha wuya a kansa, duba da halin da ƙasa ke ciki a yanzu.
“A duk tsawon rayuwarta, bai taɓa yin nadamar wani abu kamar yadda ya yi nadamar mara wa Tinubu baya ba”. inji shi.
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, Dan Bilki ya nemi afuwar jama’a, inda ya bayyana cewa abubuwan da ya yi musu alƙawarin cewa za a yi, gwamnatin APC ba ta yi ba.
Ɗan Bilki Kwamanda ya yi ƙaurin suna wajen suka da yin adawa mai zafi a tsakanin abokan hamayyar jam’iyyarsa a jihar Kano.