Ghana tana shirin kasancewa cikin ƙasashen Afirka da ke da makamashin nukiliya inda take ƙoƙarin fara gina tasharta ta nukiliya ta farko.
Ministan ma’aikatar makamashi, Dokta Robert Sogbadji, ya bayyana wurare biyu da za a yi amfani da su – ɗaya a lardin Yammacin ƙasar kuma ɗaya a lardin Tsakiyar Ƙasar, domin samar da wata babbar masana’anta da wata ƙaramar masana’anta, a wani ɓangare na matakin faɗaɗa hanyoyin samun makamashin ƙasar.
- Mutum 3 Sun Rasu, 30 Sun Makale A Karshin Kasa A Ghana
- Jami’ar Ahmadu Bello ta ƙaryata zargin ƙera makamin nukiliya a cikin jami’ar
Da yake magana a lokacin bikin karramawa na makamashi na Ghana karo na 9, Dokta Robert Sogbadji ya tabbatar da cewa an fara ayyukan shirye-shirye ciki har da matakai na sayen filaye da kuma yarjejeniyar sayen makamashi na gwamnati.
Dadkta Sogbadji ya ƙara da cewa ma’aikatar tana aiki cikin wa’adi na watanni shida domin faɗaɗa samun lantarki, inda take da niyyar samar wa kasar kashi 90 cikin 1000 na makamashi.
A watan Fabrairun shekarar 2025, Ghana ta karɓi baƙuncin tawagar bin ba’asin harkar nukiliyarta ta farko inda ƙwararru daga Pakistan da Turkiyya da Birtaniya da kuma Amurka, wadanda gwamnatin ta gayyata kuma kamfanin makamashin nukiliyar Ghana ya karɓi baƙuncinsu.
