Gwamnatin kasar nan ta ce ba za ta gajiya ba har sai ta farauto maharan da suka kashe masallata a garin Malumfashi da ke jihar Katsina.
Gwamnatin ta ce maharan sun nuna rashin imani.
Cikin wata sanarwa da ministarn yaɗa labarai Muhammad Idris ya fitar, gwamnatin tarayya za ta tabbatar an kama maharan tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
Ministan ya ce tuni jami’an tsaro suka fara bibiyar maharan, inda ya ƙara da cewa ba za su gajiya ba sai an kama waɗanda suka kai harin.
Ya ce Shugaba Tinubu na miƙa ta’aziyarsa ga iyalan waɗanda aka kashe, da mutanen Malumfashi da jihar Katsina da ma ƙasar baki ɗaya da ma iyalan waɗanda aka kashe.
Ya ce daga cikin ƙoƙarin da gwamnati ke yi na kawo ƙarshen lamarin akwai kama fitattun ƴan ƙungiyar Ansaru da ake zargi da fasa gidan yarin Kuje da sauran nasarori.
