
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Cibiyar Fasaha ta Zamani ta Arewa Maso Yamma da Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) ta gina a Kano.
Ministan Sadarwa Da Fasaha da Tattalin Arzikin Hanyoyin Sadarwa Ta Zaman, Dakta Bosun Tijani ne ya wakilci Shugaban Ƙasa a bikin ƙaddamarwar a ranar Talata.
“Cibiyar na daga cikin muhimman ayyukan shugaba Tinubu ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda da ke da nufin fitar da matasa daga kangin talauci ta hanyar fasaha”.In ji shi
Cibiyar wadda aka gina da kayan aikin zamani an lalata shi a watan Agustan 2024 yayin zanga-zangar matsin rayuwa da aka yi a shekara 2024 mako guda kafin ƙaddamar da ita.
Duk da haka, Minista Tijani ya ce, bai bari fushin lalata cibiyar ya hana ci gaba da aikin ba, inda ya tuntuɓi kamfanoni kai tsaye don gyara ta cikin gaggawa ba tare da bin dogon tsarin gwamnati ba.
A cewar ministan, cibiyar za ta horar da matasa miliyan uku a fannin fasaha da ƙwarewar dijital, domin su samu damar shiga kasuwannin duniya da kuma gina rayuwa mai inganci.
Ya kuma jaddada cewa matasa ba su da uzurin zaman banza, duba da irin damar da cibiyar ke bayarwa.
Gwamnan Jihar Kano ta bakin mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya bayyana cewa jihar na da shirin horas da matasa 300,000 kan fasahar zamani nan da shekarar 2027.
Haka kuma, an riga an horar da ma’aikatan gwamnati 5,000 da suka samu ƙwarewa a fannin fasaha, a wani bangare na shirin dijital da jihar ke aiwatarwa.