Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar ilimin bai daya (SUBEB) da hadin gwiwar Plane sun fara horas da malamai sabbin dabarun koyarwa da harshen turanci.
Karkashin shirin kashi na farko za a horas da malamai 484 da suka fito daga makarantu 115 na jihar Kano.
An zabo makarantun ne daga kananan hukumomin Takai da Gabasawa da Karaye da kuma Minjibir.
Wasu daga cikin Malaman dake karbon horon sun ce suna samun sabbin dabarun koyar da darasin turanci.
Sun ce da wannan horo da suka samu za a ga sauyi a yadda dalibai ke koyo da amfani fa harshen turanci.
Da yake karin haske shugaban kungiyar Plane a nan Kano Umar Lawan, ya ce Malaman zamu samu sabbin dabaru don inganta koyo da koyarwa.
Ya ce suna gudanar da shirinne hadin gwiwa da ma’aikatar ilimi da kuma hukumar ilimin bai daya ta Jiha (SUBEB).
Ya kara da cewa a shekaru uku da suka gabata sun bayar da makamancin wannan horo domin inganta koyarwa a harshen Hausa yayin da a yanzu suke bayarwa don inganta koyarwa da harshen turanci.
Shima matekamakin shugaban Plane na kasa Sam Acimugu, ya ce a karshen horaswa da za a karkare a ranar 18 ga Janairu Malamai zasu iya koyar da Dalibai magana da rubutu da turanci.
Ya ce wannan yayi daidai da tsarin da gwamnatin tarayya ta fito da shi na koyarwa da harshen turanci a makarantun kasar nan.
Sam, ya kara da cewa baya ga horon za kuma a basu kayan aiki.
