Kungiyar tsoffin dalibai na makarantar sakandiren Dambatta aji na 1985 sun karrama sabon shugaban jami’ar Bayero Kano Farfesa Haruna Musa da shaidar girmamawa bisa irin gudinmowar da yake bayarwa a fannin ilimi.
Farfesa ya kasance daya daga cikin mamba a kungiyar da yake jawabin godiya Farfesa Haruna Musa ya nuna matukar farin cikinsa da abin yan ajin nasu suka yimasa, inda ya bukaci su taya shi da addu’a domin sauke nauyin da aka dora masa na shugabancin Bayero.
A nasa bangaren Alh Ali Abdu Dala ya bawa shugaban jami’ar bayero shawarar mai da hankali wajen kawo ci gaban a jami’ar tare da yin kira ga sauran mambobin kungiyar sakandiren da su ci gaba da bayar da gudin mowa a makarantar da suka gama.
A nasa jawabin Dan Majen Ringim Hakimin Taura Alh Nura Usman ya yi janhankali ga wadanda suka samu kansu a shugabanci da suyi kokarin kamanta gaskiya da adalci a cikin alummar da suke wakilta.
Kungiyar tsoffin daliban makarantar sakandiren Dantabatta aji na 1985 ta gudanar da taron sada zumuncin na cikarsu shekaru 40 da kammala makarantar, taron ya samu halartar mambobin kungiyar da dama inda suka gudanar da addu’o’I da malamai da daliban da suka rasu.
