
Ƙungiyar manyan ma’aikatan manfetur da iskar gasa ta kasa (PENGASSAN) ta yi barazanar yin zanga-zanga a gaban matatar man Dangote kan zargin korar ma’aikata 800 da suka shiga ƙungiyar.
Ƙungiyar ta zargi cewa sama da Indiyawa 2,000 kamfanin ya ɗauka don su maye gurbin waɗanda aka kora ranar Alhamis.
Sai dai matatar man Dangote ta ce kaɗan daga cikin ma’aikatanta aka kora saboda maimaita munanan ayyukan lalata kayayyaki (sabotage).
A wata sanarwa kamfanin ya fitar a ranar Juma’a ta ce wannan wani sabon tsarin sake fasalin aiki ne da ya zama dole domin kare matatar daga irin waɗannan munanan ayyuka.
Sai dai shugabannin PENGASSAN sun ce an kori ma’aikatan ne saboda shiga ƙungiya.
Sakatare Janar na ƙungiyar, Lumumba Okugbawa, ya zargi cewa ma’aikatan 800 an kora su ne saboda zama mambobi na PENGASSAN.
Ƙungiyar ta yi kira ga matatar da ta dawo da dukkan ma’aikatan da aka kora, in ba haka ba za su yi amfani da doka da kundin tsarin mulki wajen kare hakkinsu.
Matatar mai ta Dangote dai ta ce tana mutunta ‘yancin kowane ma’aikaci na shiga ko kin shiga ƙungiya, tare da cewa manufar matatar ita ce ta yin hidima ga ‘yan Najeriya, ta ƙarfafa dogaro da kai a fannin makamashi, da kuma samar da ayyukan yi masu ɗorewa.
A baya-bayan nan ma, matatar ta gamu da zanga-zangar Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NUPENG) bisa zargin cewa ta hana direbobinta shiga ƙungiya amma kotu ta bayar da umarnin hana sake yin hakan.