Jam’iyyar PDP ta bayyana kudurinta na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taronta duk umarnin kotu da ya hana ta yin hakan.
kasa da aka tsara a yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba.
Hakan na zauwa ne duk da sabon umarnin kotun tarayya da ke hana ta ci gaba da shirya taron.
- Muna ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taron kasa-PDP
- Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa
Mataimakin Sakataren Yada Labarai na kasa na jam’iyyar, Ibrahim Abdullahi ne ya fadi haka a ranar Talata.
“Hukuncin kotun da ke dakatar da taron bata lokaci ne kawai, jam’iyyar na bin hukuncin da Kotun Koli ta yanke a baya wanda ke tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa suna da ikon gudanar da harkokinsu na cikin gida ba tare da tsoma bakin kotu ba”. in ji shi.
Mataimakin shugaban jam’iyar ya kuma ce, PDP ba za ta sake yarda da hukuncin da aka samo da gangan ba.
Ya kuma kara da cewa, jam’iyyar PDP ‘yan Najeriya ne suka kafa, ba kotu ba”.
Babban Kotun Tarayya karkashin mai shari’a Peter Lifu ce ta bayar umarnin dakatar da taron sakamakon karar da Sule Lamido ya shigar na hana shi takardar neman tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar.
Kotun ta ce, a dakatar da taron har sai ta yanke hukunci kan karar da tsohon gwamnan na jigawa ya shigar.
