
Jami’iyyar PDP ta yi Allah-wadai da matakin Hukumar Kula Da Birnin Tarayya Abuja (FCTA) ta yi na rufe ofishinta, kuma bayyana hakan a matsayin tauye dimokaraɗiyya.
Hukumar FCTA ta rufe babban ofishin Jam’iyyar na kasa na Wadata Plaza a ranar Litinin.
Rufe ofishin ya zo dai dai lokacin da jam’iyyar PDP ta shirya gudanar da taron masu ruwa da tsaki, a ranar, lamarin da ya tilasta dage zaman da aka tsara zuwa yau Talata.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Umar Iliya Damagun, ya bayyana cewa matakin da aka dauka na hana PDP gudanar da harkokinta ba zai yiwu ba, yana mai cewa idan ana son kama su, su a shirye suke.
A cewar jami’an FCTA sun rufe ginin ne saboda kin biyan harajin ƙasa da jam’iyyar ta yi na tsawon shekaru 20.
Rufe ofishin ya sanya jam’iyyar PDP nemi mafita ta hanyar gudanar da taronta a masaukin gwamnan jihar Bauchi da ke Abuja duk da rufe ofishin.