Jam’iyyar PDP ta sanar da ɗage tantance ƴantakarar neman shugabancin jam’iyyar zuwa wani lokacin nan gaba.
Tun farko jam’iyyar ta tsara tantance ƴantakarar ne a yau Talata, inda a ƙa’ida dukkan masu neman muƙami a jam’iyyar za su bayyana a gaban kwamiti domin a tantance su.
Daga baya, wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ta ce, sakamakon tasowar wasu muhimmai sun dole a ɗage aikin.
Kwamitin ya ce, za’a sanar da wata sabuwar ranar da za a yi tantancewar, tare da bayar da haƙuri kan rashin jin daɗin da matakin zai haifar.
Kwamitin ya ce, a shirye yake ya tabbatar da shirya babban taro mai inganci a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba a Ibadan na jihar Oyo.
