Jam’iyyar PDP ta bayyana takaici kan ficewar Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Rivers daga jam’iyyar zuwa APC ta mai mulki.
A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, PDP ta ce Fubara ya fice da kansa, kuma hakan ba zai yi wa jam’iyyar illa ba musamman a daidai lokacin da ake shirin zaben shekarar 2027.
Jam’iyyar ta kara da cewa, tun farkon rikicin da ya dabaibaye gwamnatin Rivers da PDP, al’umma sun tsaya tsayin daka wajen kare martabar jam’iyyar.
PDP ta bayyana cewa, Gwamna Fubara ba shi da dalilin ganin laifin jam’iyyar game da halin da ya shiga a jiharsa, wanda ya sa ya koma APC.
