
Jam’iyyar PDP ta nada tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Abubakar Bukola Saraki a matsayin shugaban sabon kwamitin sulhu da nufin sasanta bangarorin da ke gaba da juna a cikin jam’iyyar.
Shugaban kwamitin amintattun PDP, Sanata Adolphus Wabara, ya ce an rantsar da kwamitin mai mambobi 20 don ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a cikin jam’iyyar.
Wabara ya jaddada cewa jam’iyyar PDP na shirin kawo ƙarshen duk wata rigima da ta dabaibaye ta tun bayan kammala babban zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Ya kuma ce, jam’iyyar za ta ɗauki matakai masu tsauri kan duk wanda aka samu da laifin yin zagon ƙasa ko ɓata lissafin jam’iyya.
Cikin manyan jiga-jigan da ke cikin sabon kwamitin akwai tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau da tsohon gwamnan jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu da tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom da kuma Yakubu Garba Lado daga jihar Katsina.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Saraki ya bayyana jin daɗinsa kan yadda zaman farko na kwamitin ya gudana, yana mai cewa kwamitin zai yi aiki tukuru don tabbatar da cewa jam’iyyar ta je babban taronta cikin lumana da haɗin kai.
Jam’iyyar PDP ta sha fama da rikice-rikice na cikin gida tun bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar suka rabu da juna sakamakon sabani da rashin jituwa kan tsarin mulki da shugabanci.
Wannan sabon kwamitin na sulhu na daga cikin ƙoƙarin sake gina martabar jam’iyyar da dawo da haɗin kai tsakanin mambobinta.