
Jam’iyyar PDP ta fara kokarin shawo kan tsohon shugaban ƙasa GoodLuck Jonathan domin ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Jam’iyyar a hukumance da kuma a matakin wasu jiga jigan ta, ciki har da gwamnoni ne ke wannan yunkuri na zawarto Jonathan domin ba shi takara a jama’iyyar.
Mataimakin sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ta PDP na kasa Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da wannan yunƙuri yana mai cewa tsohon shugaban Najeriyar ya nuna yiyuwar amincewa da wannan buƙata.
Ya ce yunƙurin nasu na bai wa Jonathan takara amsa kiran da ƴan Najeriya suka yi musu ne, na dawo da tsohon shugaban saboda a yanzu an yi walƙiya kuma jama’a sun fahimci kuskuren da suka tafka a baya na ƙin zaɓen Jonathan.