
Gwamnatin tarayya ta ce kashi 31 na mata yan shekaru 15 zuwa 49 sun fuskanci cin zarafi na zahiri irinsu duka, yayin da kashi 28 suka fuskanci cin zarafi kamar fyaɗe, aƙalla sau ɗaya a rayuwarsu.
Ministar mata, Imaan Sulaiman Ibrahim, ta ce waɗannan bayanai na nuna zahiri irin halin da mata ke ciki a ƙasar nan, duk da irin ci gaba da ake samu wajen yaƙi da cin zarafin mata.
Ministar ta bayyana hakan ne a Abeokuta na jihar Ogun, yayin ziyarar aiki, inda ta ziyarci cibiyar kai ƙorafe-ƙorafen laifukan cin zarafi.
Imaan ta ce ya kamata al’umma su gane cewa cin zarafin mata ba matsala ce da ta shafi iya waɗanda ke fuskanta ba, sai dai matsala ce da ta shafi al’umma baki ɗaya, wadda kuma ke kawo tsaiko a zaman lafiya da zamantakewar iyali da kuma ci gaba.