Babban alkalin kotun Babban Birnin Tarayya Abuja, Mai shari’a Peter Kekemeke, ya bayar da umarnin kama shugaban tsagin jam’iyyar PDP na bangare, Tanimu Turaki, bayan ya ki halartar kotu domin a gurfanar da shi.
Alkalin ya bayar da wannan umarni ne bayan Turaki bai bayyana a kotu ba duk da cewa an aika masa da sammaci da takardar tuhume-tuhume da ke sanar da shi ranar zaman kotu.
Babban lauyan gwamnati, Usman Rabiu, ya bayyana cewa an shirya zaman ne domin wanda ake kara ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Ya kara da cewa duk da cewa an sanar da Turaki, bai halarci kotu ba.
Lauyan ya dogara da sashe na 396(2) na dokar gudanar da shari’ar laifuka ta shekarar 2015 (ACJA), inda ya bukaci kotu ta bayar da umarnin kamo wanda ake kara domin tilasta shi halartar kotu.
Sai dai lauyan wanda ake kara, Abdulaziz Ibrahim, ya roki kotu da ta ba shi karin kwanaki biyar domin gabatar da hujjoji kan cewa ba lallai ba ne wanda yake karewa ya halarci kotu kafin a yanke hukunci kan bukatar da suka shigar na soke karar.
A hukuncinsa, Mai shari’a Kekemeke ya ce rashin halartar kotu ba tare da wani dalili ba, duk da cewa an sanar da wanda ake kara, kuskure ne.
Ya kuma bayyana cewa ba za a saurari bukatar soke karar ba har sai bayan wanda ake kara ya bayyana a kotu ya kuma amsa tuhumar da ake masa.
Don haka, kotu ta bayar da umarnin kama Turaki domin tilasta shi bayyana a gaban kotu ya amsa tuhumar da ake masa.
An dage shari’ar zuwa ranar 22 ga Afrilu domin gurfanar da shi.
