
Onana da Shugaba Ibrahim Traore a yayin ziyarar
Mai tsaron gida na kulob din Manchester United, Andre Onana ya ziyarci shugaban kasar Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traore.
Rahotannin sun ce Onana ya ziyarci shugaban ne a Ougadugou babban birnin kasar a wata ziyara da dan wasan ke ya don halartar wasannin tara kuɗin jin-kai da gidauniyar Bertrand Traoré Foundation ta shirya.
TRT ta rawaito cewa, a yayin ziyarar Onana ya ba shugaba Traore rigar wasansa mai dauke da sunansa da kuma sa-hannunsa.
Onana ɗan asalin Kamaru ne, kuma ya bayyana godiyarsa kan tarbar da ya samu a ƙasar, ya kuma yaba wa al’adu da al’ummar ƙasar da ke Yammacin Afirka.