
Hukumar EFCC gabatar da Murja Ibrahim Kunya a kotu a inda take zargin ‘yar Tik Tok din da wulaƙanta takardar Naira
Hukumar na zargin cin karo da bidiyon jarumar tana tiƙar rawa a kan takardun kuɗi har kimanin Naira dubu 400 a watan Maris.
Hakan na kunshe ne a ƙarar da EFCC ta gabatar mai lamba FHC/KN/CS/18/2025 a gaban wata Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano tun a watan Maris, wanda aka ci gaba da sauraro a ranar Talata 15 ga watan Afrilu 2025.
Hukumar ta ce, laifin da take tuhumar Murja tanadi ne na Kundin Dokokin Babban Bankin Najeriya CBN wanda ya haramta wulaƙanta takardar Naira ta kowace siga.
EFCC ta ce, jami’anta sun binciki bidiyon wanda ya nuna ’yar TikTok ɗin na tiƙar rawa gami da liƙi da takardun kuɗi ’yan Naira 500 da 1,000 wanda jimillarsu ya kai Naira dubu 400, a otel ɗin Tahir da ke Kano.
Aminiya ta rawaito cewa, yayin zaman kotun na ranar Talata, Lauyar EFCC, Lily Jacobs ta gabatar da bidiyon a matsayin shaida tana mai roƙon kotun da ta yanke hukunci daidai da abin da Murjar ta aikata.
Sai dai bisa dogaro da sassa na 274 da 356 na kundin tsarin shari’ar laifuka alkalin kotun ta nemi EFCC ta gabatar da tarkardar kuɗin Naira dubu 400 a matsayin shaida amma ta gaza ta kuma buƙaci a ba ta lokaci.
Alƙalin ya bayyana cewa akwai nauyin da rataya a wuyansa na bai wa kowane bangare kariya tsakanin masu ƙara da wanda ake tuhuma, inda ya bayyana cewa shaidar da EFCC ta gabatar ba ta zama cikakkiya ba.