Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a garin Isapa a karamar hukumar Eikiti a jihar Kwara, inda suka yi garkuwa da mutane 11 ciki har da wata mata mai juna biyu da kananan yara.
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kai akalla mutum 20 zuwa 30 da suka mamaye wasu sassa na garin kafin su sace waɗanda suka haɗa da mata da yara.
Shugabannin al’umma a yankin sun tabbatar da cewa cikin wadanda aka sace akwai mutane 11, ciki har da kananan yara bakwai daga cikinsu ‘yan gida daya.
Ciki wadanda yan bindigar suka sace sun haɗa da Talatu Kabiru, Magaji, Kande, Hadiza, Mariam, Saima, Habibat, Fatima Yusufu, Sarah Sunday, wadda ke ɗauke da juna biyu, Lami Fidelis, ma’aikaciyar lafiya, da Haja Na Allah.
