
Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE) reshen Kano ta ja hankalin mambobinta kan mutunta aiki da zuwa wurin aiki akan lokaci da riƙe sirrin ofis.
Shugaban reshen, Comrade Ibrahim Muhammad, ya yi wannan kira yayin ziyara da suka kai ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a ranar Laraba.
Ya ce zuwa wurin aiki akan lokaci zai taimaka wajen farfaɗo da ingancin ayyuka a ƙananan hukumomi 44.
Haka kuma, Comrade Ibrahim ya bayyana cewa akwai tsare-tsare na koyawa ma’aikatan da suka kusa ritaya sana’a ko bita, domin su samu rayuwa mai inganci bayan barin aiki.