Gwamnatin Pakistan ta yi barazanar kai hari kan Afghanistan, bayan fashewar wani bam da ya auku a wajen ginin wata kotu da ke Islamabad, babban birnin ƙasar.
Ministan Harkokin Tsaro na ƙasar, Khawaja Muhammad Asif, ne ya bayyana hakan, inda ya ce wannan mataki na iya zama martani ga hare-haren da ake kai wa ƙasar daga iyakokin Afghanistan.
Asif ya ce hare-haren da ake kai wa Pakistan suna ƙara zama barazana ga tsaron ƙasar da al’ummarta gaba ɗaya
Dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, Pakistan da Afghanistan, na kara taɓarɓare a ‘yan watannin da suka gabata.
Pakistan na zargin ’yan Taliban na Afghanistan da bai wa ƙungiyoyin ’yan bindiga mafaka, da kuma kitsa hare-hare a iyakokin Afghanistan.
Sai dai gwamnatin Taliban ta ƙaryata wannan zargi.
