Tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kudurori guda huɗu na #GyaranHaraji ga majalisar dokoki na ƙasa a watan da ya gabata, an samu ce-ce-ku-ce da yawa da suka mamaye muhawarar kan waɗannan kudurorin. Yawancin waɗannan ce-ce-ku-ce suna fitowa ne daga rashin fahimtar waɗanda ke tayar da jijiyoyin wuya don yin nazarin abubuwan da kudurorin suka ƙunsa. A sakamakon haka, talakawan ‘yan Najeriya da yawa suna cikin ruɗani game da ainihin matsayin waɗannan kudurori, musamman yadda za su shafi aljihunsu.
Zan yi ƙoƙarin yin bayani kan kudurorin gyaran haraji cikin sauƙi da gajeren bayani.
Waɗannan kudurorin gyaran haraji guda huɗu suna da nufin tsara dukkan harkokin haraji a Najeriya cikin sauƙi, ta hanyar yin amfani da dokoki huɗu. Ga jerin kudurorin:
- Dokar Haraji ta Najeriya
- Dokar Gudanar da Haraji ta Najeriya
- Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Najeriya
- Dokar Kafa Hukumar Haɗin Gwiwar Haraji
Dokar Haraji ta Najeriya
Wannan doka ita ce inda dukkan manyan haraji da ake caji kan kamfanoni da mutane za a bayyana da kyau, tare da adadin kuɗin harajin. Wannan dokar za ta haɗa dukkannin tsofaffin dokokin da suka tanadi cajin haraji a Najeriya, inda za a soke dokoki 11 da ke da alaƙa da haraji idan an amince da ita.
Wasu daga cikin muhimman abubuwan da wannan doka ta ƙunsa sun haɗa da:
- Rage haraji ga masu karɓar albashi na N800,000 ko ƙasa da haka a shekara. Yanzu haka, masu karɓar wannan adadi suna biyan N84,000 a matsayin haraji. Sabuwar dokar za ta fitar da su daga biyan komai.
- Masu samun fiye da N50 miliyan ne kawai za su biya harajin kashi 25%. A yanzu, duk wanda ya samu sama da N3.2 miliyan na shekara yana biyan kashi 24% na kudinsa a matsayin haraji.
- Kanana da matsakaitan kamfanoni za su samu sassauci daga biyan haraji. Kamfanoni da ke da kudaden shiga na N50 miliyan ko ƙasa za su samu ‘yanci daga haraji, maimakon tsohon tsarin da ya takaita wannan sassaucin ga kamfanoni da ke samun N25 miliyan ko ƙasa.
- Rage harajin kamfanoni daga kashi 30% zuwa kashi 25% daga shekarar 2026.
- Rashin caji kan manyan kamfanonin da ba su bayyana riba ba. Haraji zai takaitu ne ga ribar da aka samu kawai.
Dokar Gudanar da Haraji ta Najeriya
Wannan dokar tana tanadar yadda hukumomin haraji za su gudanar da ayyukansu. Ta kuma fayyace ayyukan hukumomin haraji da yadda za a gudanar da tarin kudade da sauran ayyuka masu alaƙa.
Wasu daga cikin abubuwan da dokar ta ƙunsa sun haɗa da:
- Tsaida masu wadata daga gujewa biyan haraji. Wannan yana tabbatar da cewa waɗanda ke da ma’amala sama da N25 miliyan (mutum) ko N100 miliyan (kamfani) a wata guda, bankuna za su kai rahotonsu ga hukumar haraji.
- Biyan haraji a Naira. Wannan zai taimaka wajen inganta darajar Naira.
- Karɓar haraji daga kamfanonin da ke gudanar da ayyuka ta hanyar dijital.
- Raba kudin VAT bisa amfani da maƙasudin asali. Wannan tsarin zai bai wa jihohin da ba su da hedikwatar kamfanoni babban rabo daga kudin VAT.
Muhimmancin Kudurorin
Waɗannan kudurori na gyaran haraji suna nufin inganta tsarin haraji a Najeriya, rage wahalhalu ga talakawa da kanana, tare da bai wa manyan kamfanoni damammaki masu kyau. Kowa ya kamata ya goyi bayan waɗannan kudurori domin ci gaban kasa.
Engr. Mohammed Awal Ibrahim
Sugabar kungiyar taya PBAT GCFR nemar nasar zabe.
Global coordinator TSGSG(Tinubu Shetima Global support group)