
Hukumar kula da Jiragen Kasa ta Kasa (NRC) ta bayyana musabbabin hadarin jirgin ƙasa da ya afku a hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar 26 ga watan Agusta.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Alhamis.
Sanarwa wacce Shugaban Hukumar Kayode Opeifa ya sanya wa hannu, sakamakon cikakkaken bincike ne da wani kwamitin bincike ya yi don gano dalilan da jirgin ya sauka daga layin dogo, wanda hakan ya sa mutane 21 daga cikin fasinjoji 618 da ke cikin jirgin suka samu raunuka.
Rahoton kwamitin ya bayyana cewa hatsarin ya samo asali ne daga kuskuren ɗan’adam, musamman tsananin gudu da kuma rashin kwarewa wajen sarrafa birkin jirgin daga bangaren matuƙin.
“Binciken kwamitin da muka kafa ya tabbatar da cewa ba wata matsala ta fasaha da aka samu a tsarin jirgin ko hanyarsa, illa dai rashin bin ka’idojin tuki da kuma gaggawa wajen sarrafa jirgin lokacin da ake bukatar hakan.” In ji sanarwar.
Hukumar NRC ta kuma ce, tuni aka fara aiwatar da wasu daga cikin shawarwarin da aka bayar a cikin rahoton.