Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Najeriya (NOA) ta jaddada kudirinta na ƙarfafa haɗin kan ‘yan ƙasa da nufin gina kishin ƙasa a tsakanin al’umma.
Daraktan hukumar na ƙasa, Malam Lanre Issa-Onilu, wanda Daraktan Sashen Ayyuka na Musamman, David Akoji, ya wakilta, ya bayyana hakan a wani shirin bada horo kan kishin ƙasa da girmama ta.
Mista Akoji ya ce shirin na daga cikin manyan ayyukan ƙasa da zai taimaka wajen wayar da kan ‘yan ƙasa game da haƙƙoƙinsu da nauyin da ke kansu, tare da inganta jagoranci a wuraren aiki.
Shirin ya nuna ci gaban haɗin gwiwa tsakanin NOA da abokan ta domin gina ingantaccen alamar ƙasa da kuma haɓaka jagoranci nagari a hukumomi da sassa daban-daban na ƙasar.
