
Hukumar wayar da kan al’umma ta kasa NOA reshen jihar Kano ta bukaci ‘yan kasar dasu kasance masu nuna kishin kasa, kaunar juna, da sadaukarwa ga kasar su.
Daraktan hukumar na Kano Alhaji Rabi’u Ado ne ya bayyana hakan ta cikin sakon hukumar na taya ‘yan kasar murna samun ‘yancin kan, inda yace babu wata kasa da zata zauna lafiya da samun ci gaba ba tare da kaunar juna da kishi daga ‘yan kasar ba.
Rabi’u Ado ya ce, sabon shirin kyakkyawan fata na Shugaba Bola Ahmad Tinubu wato renewed hope Agenda, da ragowar tsare-tsare, ansamar da su ne da nufin bunkasa walwalar ‘yan kasa kasancewar gwamnati ta dauki fanni tsaro da walwalar ‘yan kasa a mataki na farko a tsarin Mulkin ta.
Da yake yiwa wakilin mu Kamal Umar Kurna karin bayani kan muhimmancin ranar samun ‘yancin, daraktan hukumar ta NOA Kano Alhaji Rabi’u Ado, ya ce hakki ne, wanda kuma ya zamo wajibi akan kowane dan kasa ya samu ilimin sanin najeriya domin zamowa mai kishin ta.
Alhaji Ado ya kuma yabawa ‘yan mazan jiya wadanda suka jajirce matuka domin ganin najeriya ta samu ‘yanci da kasancewa kasa mai cikakken ‘yancin cin gashin kanta.