
Shugaban haramtaciyyar kungiyar Biafra ta IPOB, Nnamdi Kanu, ya kori dukkan lauyoyinsa tare da bayyana cewa zai kare kansa da kansa a gaban kotu.
Shugaban haramtaciyar kungiyar fafutukar ‘yancin Biafra IPOB yayi ikirarin kare kansa kan tuhumar da gwamnati take masa na aikata laifukan ta’addanci.
A lokacin zaman kotun da aka gudanar a yau Alhamis, babban lauyan Kanu, Sanata Kanu Agabi (SAN), ya sanar wa da kotu cewa shi da sauran manyan lauyoyin Kanu sun janye daga kare shi a wannan shari’ar.
Mai shari’a James Omotosho ya amince da bukatar janyewar lauyoyin.
Yayin da alƙalin ya tambayi Kanu ko yana da sabon lauya da zai kare shi, sai Kanu ya amsa da cewa zai tsaya domin ya kare kansa, baya buƙatar lauya.” Daga nan sai Mai shari’a Omotosho ya umurci sauran ƙananan lauyoyi ba da su bar dakin kotu.
A halin yanzu, Nnamdi Kanu ya saka sunayen tsofaffi da kuma wasu jami’an gwamnati masu aiki a matsayin shaidu da zai gabatar wajen kare kansa.