Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta sanar da gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya a ranar 17 ga watan Disamba, sakamakon yadda matsalar tsaro ke ta’azzara a sassa daban-daban na kasar.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana haka cikin wata sanarwa bayan taron masu ruwa da tsaki na kungiyar da aka gudanar a daren Litinin a Lagos.
Kungiyar ta nuna damuwa kan harin ’yan bindiga da ya yi sanadin sace dalibai mata 24 a Jihar Kebbi, lamarin da ta ce ya faru ne bayan an janye jami’an tsaro da ke gadin makarantar.
A cewar NLC, yawaitar hare-haren garkuwa da dalibai a kwanakin nan abin tashin hankali ne, wanda ya zama dole gwamnati ta dauki matakai na gaggawa domin dakile matsalar tsaro a fadin kasa.
Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatocin jihohi da hukumomin tsaro su kara ba fannin tsaro muhimmanci, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
