Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a ranar Talata kan karin kudin kiran waya da kuma data.
A makon da ya gabata, NLC ta yi barazanar fita zanga-zanga matukar gwamnati da kamfanonin sadarwa ba su janye karin kudin ba.
Sai dai bayan wata ganawa da shugabannin NLC da wakilan gwamnati a daren jiya Litinin, an cimma matsaya kan dakatar da yajin aikin.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da kafa kwamitin da zai duba karin kudin.
Kwamitin zai kunshi wakilai biyar daga kowanne bangare kuma zai gabatar da rahoto cikin mako biyu.
Ajaero ya ce sakamakon rahoton zai bayyana matakin da NLC za ta dauka nan gaba.