Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da bayar da umarnin kwace mata fasfo a filin jirgin sama.
Lamarin ya faru ne a safiyar yau Talata ta hanyar wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Facebook.
Sanatar ta bayyana cikin fushi yayin da take cece-kuce da jami’an Hukumar Shige Da Fice Ta Kasa (NIS), da tace sun riƙe mata fasfo kan hayarta na fita waje.
“Wannan ba shine karon farko da aka yi irin wannan ba, domin Akpabio ya sha zargina da ɓata wa ƙasa suna duk lokacin da ta fita ƙasashen waje.
“Babu wani umarnin kotu da ya halatta hakan. Na kuma tunatar da jami’an cewa Shugaba Bola Tinubu ya taɓa umartar Akpabio da ya dakatar da duk wani mataki da ake ɗauka a kaina”. In ji ta.
Bayan shafe wani lokaci, wani jami’in hukumar shige da fice ya dawo mata da fasfo ɗin nata.
Har yanzu, ofishin Akpabio da Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa ba su fitar da wata sanarwa ba kan lamarin.
