Aminu Abdullahi Ibrahim
Cibiyar yada labarai da hulda da jama’a ta ƙasa (NIPR) ta kai ziyara jihar Kano domin duba wasu muhimman ayyuka da gwamna Abba Kabir Yusuf ke gudanarwa.
Shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Mr. Ike Naliaku, ne ya jagoranci tawagar, inda suka nuna sha’awa matuƙa kan ayyukan da gwamnati ta sanya a gaba domin bunƙasa rayuwar al’umma.
Wannan na daga cikin shirye-shiryen da cibiyar ke yi na nada Abba Kabir Yusuf amatsayin uban cibiyar ta NIPR.
Tawagar ta fara ziyarar ne a wajen aikin gadar sama ta Dan’agundi, wanda ake sa ran zata magance cunkoson ababen hawa da ake fuskanta.
Daga nan, tawagar ta zarce zuwa unguwar Gayawa, inda suka shaida irin matsalar zaizayar ƙasa da ke addabar al’umma, tare da jin ra’ayin jama’a kan matakan da ake ɗauka.
Haka kuma, kungiyar ta duba gidajen gwamnati na Kwankwasiyya, kafin su kai ziyara zuwa Chalawa Dam da ke karamar hukumar Karaye, domin ganin irin cigaban da ake samu wajen samar da wuta ga al’umma jihar kano.
A yayin ziyarar, gwamnatin Kano ta samu wakilcin Daraktan yada Labarai na gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya bayyana wa tawagar cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da aiwatar da manyan ayyuka da suka shafi jin daɗin al’umma.
Shugaban NIPR, Mr. Ike Naliaku, ya jinjinawa gwamnatin bisa yadda take aiwatar da ayyuka, inda ya ce hakan na nuna kishin kasa da manufar kawo sauyi ga rayuwar jama’a.

