Gwamnatin Nijeria ta mayar wa shugaban jamhuriyar Nijar martani kan zargin ta ba Faransa izinin kafa sansani a arewacin kasar.
Hakan na cikin wata sanarwa da Mataimaki Na Musamman Kan Yada Labarai Da Sadarwa ga Ministan Harkokin Wajen kasar Alkasim Abdulkadir ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwa ta kuma kara da cewa Zargin da shugaba Abdurrahman Tchiani ya yi a wata da wani gidan talabijin a Yamai, babban birnin kasar na ranar Kirsimeti ba gaskiya kuma yaudara ce.
“Babu wani sansanin kasar Kanada da sojojin Faransa a jihar Borno. Abu mafi muhimmanci shi ne, babu wani sojan Faransa a Najeriya ko wani shiri da gwamnatin Najeriya da ke yi na kafa ofishin soja da Faransawa ke rike da su” Inji sanarwar.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya je birnin Paris ne, inda kuma ya rattaba hannu kan yarjejeniyoyin biyu, na bunkasa ababen more rayuwa ne da samar da abinci.
Yarjejeniyoyin sun kuma hada da shirin zuba jari na Euro miliyan 300 don tallafa wa harkar kiwon lafiya da sufuri da noma da makamashi a fadin Najeriya.
Don haka ba za a musanya kudaden don kafa sansanonin soja ba.
Har ila yau, muna sake nanatacewa, babu wani sabani a cikin dangantakar Najeriya da Faransa. Yana da kyau a bayyana cewa a ko da yaushe alakar Najeriya da Faransa tana da kyau, kuma suna mutunta juna, da rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na juna.
Faransa da Jamhuriyar Nijar sun raba gari ne tun lokacin da sojoji suka kwace mulki a kasar. Shugabannin na soji sun kuma warware duk wasu yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka kulla.
Wanda hakan ya sa ta korar sojojin na Faransa daga Nijar.